Trending

Yadda Ake Duba NECO Result 2026 Online

An fitar da sakamakon jarabawar NECO SSCE Internal 2026, kuma ɗaliban da suka rubuta jarabawar za su iya duba sakamakonsu ta yanar gizo. Ga yadda ake duba NECO result 2026 ta hanyar amfani da shafin NECO na hukuma.

Abubuwan Da Ake Bukata Kafin Duba NECO Result

Kafin ka fara duba sakamakonka, ka tabbatar kana da:

  • NECO Registration Number
  • NECO Result Checking Token
  • Wayar hannu ko kwamfuta mai haɗin intanet.

Yadda Ake Duba NECO Result 2026

1. Shiga shafin NECO na duba sakamako

Buɗe browser a wayarka ko kwamfuta sannan ka shiga shafin NECO na hukuma:

NECO Result Portal

2. Zaɓi shekarar jarabawar

A wajen Examination Year, zaɓi 2026.

3. Zaɓi nau’in jarabawar

A wajen Examination Type, zaɓi nau’in jarabawar da ka rubuta. Ga ɗaliban da suka rubuta jarabawar SSCE ta makaranta ta 2026, zaɓin da ya dace shi ne SSCE INTERNAL.

4. Shigar da Token

Rubuta NECO Result Checking Token ɗinka a wurin da aka tanada.

5. Shigar da Registration Number

Sannan ka rubuta NECO Registration Number ɗinka a akwatin da aka tanada.

6. Danna “Check Result”

Bayan ka tabbatar da bayanan da ka shigar sun yi daidai, danna Check Result. Idan komai ya yi daidai, sakamakonka zai bayyana a shafin.

Ba Ka Da NECO Result Token?

Idan ba ka da token, shafin NECO yana da zaɓin Purchase Token wanda za ka iya amfani da shi wajen sayen token ɗin duba sakamako. Masu account za su iya shiga ta Login, yayin da sabon mai amfani zai iya ƙirƙirar account daga shafin.

Muhimmin Bayani

Ka tabbatar kana amfani da official NECO result portal wajen duba sakamakonka, kuma ka yi hattara da wasu shafukan yanar gizo da za su iya neman bayananka ko kuɗinka ba tare da ka tabbatar da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button