“An Bashi Sabuwar Waya da ₦50k a Take” – Yadda Alh. Saud Inuwa Ya Canzawa Matashin Mai Zane Rayuwa

Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya ɗauki hankulan ƴan Najeriya, bayan da ya nuna yadda wani matashi mai fasahar zane a garin Abuja ya samu kyautar ban mamaki daga wani sanannen ɗan kasuwa.
A cikin bidiyon wanda ya bazu a dandalin TikTok, an gano mai zanen mai suna Mr. Ahmed Suleiman (wanda aka fi sani da Mr Ahmed The Speed Artist) yana zana fuskar Alh. Saud Inuwa.
Fasahar Zane a Cikin Ofis
Matashin wanda ya shahara wajen zana fuskar mutum a ƙasa da mintuna biyar, ya nuna kwazonsa kai tsaye a gaban shugaban rukunin kamfanonin na Saud Groups of Companies.
“Mr. Ahmed ya burge Alh. Saud matuƙa da fasaharsa yayin da yake zana shi a cikin ofishinsa.”
Ya Bashi Kyautar Waya Da ₦50,000
Cikin jin daɗin fasahar da matashin ya nuna, Alh. Saud Inuwa ya nuna karamci na ban mamaki. Ya ce: “Cikin jin daɗi da kuma nuna goyon baya ga basirar matashin, Alh. Saud Inuwa ya yanke shawarar sanya masa murmushi a fuska inda ya ba shi kyautar sabuwar wayar hannu da kuma tsabar kuɗi har Naira 50,000 a take.”
An jiyo wani matashi mai suna Kimzzy, wanda shi ne silar haɗa mai zanen da shugaban kamfanin, yana nuna tsananin murnarsa tare da yin jinjina ga Alh. Saud bisa wannan alheri.
Martanin Jama’a A TikTok
Al’umma da dama a shafin TikTok sun bayyana jin daɗinsu game da wannan al’amari, inda suka riƙa yi wa mai zanen murna. Wata mai amfani da shafin mai suna Ayorka ta nuna jin daɗinta inda tace: “Na aminta da kai ɗan’uwana, Allah ya yi albarka. Muna son ganin irin waɗannan abubuwan masu yawa.”
Ita kuwa Ms Dara cewa ta yi: “Naji matuƙar farin ciki da girmansa ya fara bayyana. Wannan shi ne farkon ɗaukakarka.”
Wani mai suna Halhassanzy ya ƙara da cewa: “Jinkirin ƙaddara ba yana nufin an hanaka ba ne. Masha’Allah, ina taya shi murna sosai.”
Kalli bidiyon a ƙasa;





