Entertainment

RR Production Ta Sanar Da Fitowar Sabuwar Waƙar “Abadan Daiman”

Kamfanin RR Production ya sanar da cewa sabuwar waƙar fim mai suna “Abadan Daiman“, wadda Abdul Hassan da Murja Baba suka rera, za ta fito yau da ƙarfe 8:00 na dare a tashar YouTube ta RR Production. Sanarwar ta zo ne bayan waƙar “Abadan” ta farko ta samu karɓuwa sosai a tsakanin masoya fina-finan Hausa, musamman a TikTok, inda mutane da dama suka yi amfani da ita a bidiyoyinsu.

A cikin sanarwar da RR Production ta wallafa, kamfanin ya buƙaci masoya su shirya domin sauraron cikakkiyar waƙar Abadan Daiman, tare da gayyatarsu su yi subscribing zuwa tashar YouTube ɗinsu domin kasancewa cikin na farko da za su kalla.

Waƙar dai Abdul Hassan da Murja Baba ne suka rera, kuma tun bayan fitowar gajeren ɓangaren waƙar, mutane da dama sun fara bayyana ɗokin jin cikakkiyar waƙar.

A comments kuwa, an ga mabiya da dama suna rubuta kalamai kamar:

  • “Can’t wait!”
  • “Kun shirya saka mu wani sabon kuka kenan.”
  • “Abadan ta farko ta yi mana daɗi, muna fatan wannan ma za ta kayatar.”

Wasu ma sun bayyana cewa tun bayan jin preview ɗin waƙar suka fara jiran ranar fitowarta, yayin da wasu ke hasashen cewa Abadan Daiman za ta iya sake zama wata waƙar da za ta yi fice a TikTok kamar yadda waƙar Abadan ta farko ta yi.

Yayin da ake ci gaba da jiran fitowar cikakkiyar waƙar, alamu sun nuna cewa masoya RR Production da masu kallon fina-finansu suna da babban fata kan Abadan Daiman, musamman ganin irin karɓuwar da waƙar Abadan ta samu a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button