Adam A. Zango Ya Bayyana Dalilin Rabuwarsa Da Matarsa Maimuna Pretty

Bayan ce-ce-ku-cen da suka bazu a kafafen sada zumunta kan rabuwar aurensu, fitaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango ya fito ya tabbatar da cewa shi da matarsa Maimuna Pretty sun rabu.
Jarumin ya bayyana cewa dalilin rabuwar tasu shi ne kasancewar su duka suna da genotype AS, tare da roƙon mutane da kada su yaɗa jita-jita ko ƙirƙirar wasu dalilai na daban.
Adam A. Zango Ya Yi Bayani
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Adam A. Zango ya bayyana cewa:
“Gaskiya ne cewa mun gano ni da ita muna da genotype iri ɗaya, wato AS. Ina roƙon kowa kada ya mayar da wannan batu abin ce-ce-ku-ce ko ya riƙa yaɗa bayanan da ba su da gaskiya. Ina so ne kawai masoyana su fahimci dalilin da ya sa aurenmu ya zo ƙarshe, tare da mutunta sirri da mutuncin kowa.”
Ya kuma bayyana cewa bidiyon da ya wallafa an ɗauke shi ne a ranar da Maimuna Pretty take barin gidansa cikin kwanciyar hankali. cewa bidiyon da ya wallafa an ɗauke shi ne ranar da Maimuna Pretty take barin gidansa cikin kwanciyar hankali.
Martanin Jama’a
Bayan wannan bayani, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.
Wasu sun yi wa Adam A. Zango da Maimuna Pretty addu’ar Allah Ya maye musu da mafi alheri tare da fatan Allah Ya ba su juriyar wannan jarabawa.
Sai dai wasu kuma sun tambayi dalilin da ya sa ba a tabbatar da genotype kafin a ɗaura aure ba, yayin da wasu suka ce ko da ma’aurata duka AS ne, yana da muhimmanci su nemi shawarwarin ƙwararrun likitoci kafin yanke irin wannan hukunci.
Ya Buƙaci A Mutunta Sirrinsu
Adam A. Zango ya kuma roƙi masoya da masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yaɗa jita-jita ko ƙirƙirar wasu bayanai marasa tushe game da rabuwar aurensu.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne a mutunta mutunci da sirrin dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
Bayan bayanin da Adam A. Zango ya fitar da kansa, batun rabuwar aurensa da Maimuna Pretty ya ci gaba da zama abin tattaunawa a kafafen sada zumunta. Duk da mabambantan ra’ayoyin da mutane suka bayyana, jarumin ya jaddada cewa yana fatan mutane za su mutunta sirrinsu tare da gujewa yaɗa bayanan da ba su da tabbaci.


