Trending

‘Kayi Mana Addu’a Muma Muje Madina’ – Bidiyon Bilal Villah A Kusa Da Ka’aba Ya Ratsa Zukatan Masoya

Bidiyon fitaccen mawaƙin Hausa, Bilal Villah, sanye da tufafin harami yana gudanar da addu’a cikin ƙasƙantar da kai a kusa da Ka’aba da ke birnin Makkah, ya sami karɓuwa sosai a tsakanin masoyansa a kafar TikTok.

A cikin bidiyon mai tsawon minti guda, an hango mawaƙin yana roƙon Allah arziƙi, shiriya, da sauran buƙatu na alheri, wanda hakan ya jawo martani da addu’o’i masu yawa daga masoya.

Martanin Masoya a TikTok:

Bayan wallafa bidiyon, dubban mabiya ne suka cika shafin da addu’o’i da kalmomin godiya. Daga cikin sharhin da mutane suka rubuta akwai:

  • “Allah ya karɓi ibada ya samunada rabon zuwa.”
  • “Wallahi burina na je Madina.”
  • “Allah ya nuna mana muma mun je.”
  • “Ameen ya Allah, Masha Allah Bilal akwai ilimi.”

Mafi yawan mutane sun nuna sha’awarsu da roƙon Allah na samun damar gudanar da ibada a Makkah da ziyartar gidan Annabi (SAW) a Madina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button