“Ya Biya ₦150k Don Ayi Masa Kwalliya” – Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Koma

Wani al’amari mai ban mamaki ya dauki hankulan masu amfani da shafukan sada zumunta, musamman TikTok, bayan wani matashi ya ziyarci shagon kwalliya da nufin a yi masa kwalliya irin ta mata.
Kwalliyar Naira 150,000
A cikin bidiyon, wanda ya bazu kamar wutar daji, an jiyo matashin yana tattaunawa da mai shagon inda ta tambaye shi ko zai kawo wata ne a yi mata kwalliyar. Cikin kwarin gwiwa, ya bayyana mata cewa shi za a yi wa kwalliyar, kuma yana son tsarin kwalliya na Naira 150,000.
“A’a, ina yi mana. Mu da muke neman kudi… nayi miki tsoka ai,” cewar matashin lokacin da ake tambayarsa dalilin yin wannan kwalliya.
Canjin Da Ya Girgiza Mutane
Bayan an kammala kwalliyar, wanda ya hada har da daura masa kallabi, matashin ya zama kamar wata cikakkiyar mace. A lokacin da aka bashi madubi don ya kalli kansa, ya saki salati yace: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un… gaskiya ne, duba dubu dari da hamsin dina ba’a banza ba,” yana mai bayyana gamsuwarsa da aikin.
Martanin Jama’a A TikTok
Wannan bidiyo ya janyo cece-kuce da tsokaci daban-daban daga al’umma a kafar TikTok.
Wani mai suna GONI HARUN2 yace: “Mun rasa wannan Successfully.”
Ita kuwa Ameerah collections cewa ta yi: “Subhanallah Wai daman ba content bane? dagaske yakeyi.”
Wasu kuwa cewa suke yi da alama a jihar Kano abin ya faru, inda wani mai suna Babba0272 yace: “Kano ko,” yayin da PAPILO ya nuna alhinin sa da cewa: “Ubangiji Allah yasa a tashi duniya juma’a mai zuwa.”
Kalli ainihin bidiyon a ƙasa;





