Entertainment

Abba Hikima Ya Ce Alakanta Mutum Da Shan Kwaya Ko Hauka Ba Adawar Siyasa Ba Ce

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, lauya Abba Hikima ya soki irin kalaman da ake amfani da su a siyasa wajen alakanta mutum da shan ƙwaya, giya ko hauka.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan sabuwar waƙar siyasa da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fitar, wadda mutane da dama suka danganta da Farfesa Isa Ali Pantami, bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Gombe.

“Ba Adawar Siyasa Ba Ce”

A cikin saƙon nasa, Abba Hikima ya rubuta cewa:

“Alakanta mutum da shan kwaya, shan giya ko hauka, ba adawar siyasa bace. Keta mutunci ne da cin zarafi karara kuma lallai ya kamata Sheikh Pantami ya dauki mataki akansa. Siyasa ba hauka bace.”

Wannan dai shi ne ra’ayin da lauyan ya bayyana a shafinsa na Facebook, wanda ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta.

Karanta: Soja Boy Ya Yi Martani Ga Adam A. Zango, Ya Ce “Ka Fi Kowa Daukaka Amma Ka Fi Kowa Talauci A Kannywood

Martanin Jama’a

Bayan wallafar saƙon, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu.

Wasu sun goyi bayan Abba Hikima, inda suka ce abin da ya faɗa gaskiya ne, kuma cin mutunci bai kamata ya zama wani ɓangare na siyasa ba. Wasu ma sun bayyana cewa idan Pantami ya ga dama, yana da damar ɗaukar matakin shari’a.

Sai dai a gefe guda, wasu masu sharhi sun yi nuni da cewa Rarara bai ambaci sunan Pantami kai tsaye ba a cikin waƙar, don haka suna tambayar ko akwai hujjar cewa kalaman sun nufi shi.

Muhawarar Ta Ci Gaba

Batun ya ci gaba da jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke kallon kalaman da aka yi a matsayin cin mutunci da ya kamata a guje masa, yayin da wasu kuma ke ganin suna cikin salon zambo da habaicin siyasa da aka saba gani a fafatawar siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button